in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sassanta 'yan kasar Cote d'Ivoire ba ya fatan sake ganin rikicin zaben 2010
2015-10-21 10:55:05 cri

Shugaban kwamitin sassantawa na kasa da biyan diyya ga wadanda bala'i ya shafa (CONARIV), babban malamin coci Paul Simeon Ahouana, ya bayyana a ranar Talata a birnin Abidjan cewa, hukumarsa ba ta fatan sake ganin irin rikicin gabanin zabe na shekarar 2010 da Cote d'ivoire ta yi fama da shi sosai.

Da yake isar da wani sako zuwa al'ummomin kasar a gabanin zabukan shugaban kasa da aka tsai da shirya a ranar 25 ga watan Oktoba, mista Ahouana ya gayyaci 'yan kasar Cote d'Ivoire da su nuna kishin kasa domin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.

Yana da mujimmanci a dauki dukkan matakan da suka dace domin kiyaye zaman lafiya ta hanyar zabuka cikin lumana, in ji shugaban kwamitin CONARIV.

Haka kuma, Paul Simeon Ahouana, ya yi kira ga al'ummomin kasar da su dubi tarihi na baya bayan nan a Cote d'Ivoire domin daukar darussa.

Zabuka sun kasance tamkar wata jarabawa domin nuna karfin jurewa tashin hankali, sannan kuma wata jarabawa domin nuna cewa, muna iya gina tsarin domakaradiyya da kasa mai 'yanci, in ji mista Ahouana.

Haka zalika, shugaban CONARIV ya yi kira ga kowa da kowa a kasarsa da su kaucewa Cote d'Ivoire tashin hankalin zubar da jini.

Manyan mutane kusan goma ne da suka hada da shugaban kasa mai barin gado, suna takakar zaben shugaban kasar Cote d'Ivoire da zai gudana a ranar 25 ga watan Oktoban da muke ciki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China