A ranar Labara, kasar Sin da kasar Kenya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar rancen kudi na kimanin dalar Amurka miliyan 17 domin gina manyan ayyuka uku a kasar Kenya, wadanda suka hada da mayar da 'yan gudun hijirar Somaliya zuwa kasarsu.
Rabin rancen kudin kuma za a yi amfani da shi wajen gina cibiyar Confucius mafi girma a nahiyar Afrika da za ta kasance a cikin ginin jami'ar Nairobi, in ji sakataren bitulmalin kasa, Henry Rotich a yayin wani taron manema kabarai a babban birnin kasar Kenya.
Cibiyar Confucius za ta kasance wani muhimmin dandali wajen watsa al'adun kasar Sin a kasar Kenya, da ma Afrika baki daya, in ji mista Rotich a bikin rattaba hannu. (Maman Ada)