Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Uganda ta yi barazanar dakatar da babban club din kasar a ci gaba da gasar share fage ta AFCON ta shekarar 2017, wadda aka fara a sakamakon matsalar karancin kudade.
Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Moses Magogo ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a ranar Litinin cewar, tawagar 'yan wasan na bukatar zunzurutun kudi da ya kai dalar Amurka dubu 210 kafin nan da ranar 5 ga watan Satumba domin ci gaba da gasar.
Magogo ya kara da cewar, sun mika bukatar neman kudade ga gwamnati tun watanni masu yawa da suka shude, kuma 'yan kudaden da ke hannusu ya kare, a don haka ba su da wani zabi illa kawai su kauracewa shiga gasar, idan har ba'a samar musu da kudaden ba. Hukumar wasanni ta kasar dai na zaman zulumi na neman kudaden gudanarwa daga gwamnatin.
A yanzu haka, kasashen Uganda da Burkinafaso na kan gaba a rukunin "D" na wasan share fagen gasar AFCON ta shekarar 2017 bayan da kowannensu ta yi nasara da ci 2 da nema a wasan da suka buga da Bostswana da Comoros. (Ahmad Fagam)