Rundunar 'yan sandan Uganda ta bayyana cewa, nan ba da dadewa ba za ta gurfanar da jagoran 'yan tawayen ADF Jamil Mukuku a gaban kuliya don amsa zargin da ake masa na kashe wasu jagororin musulumi.
Shugaban 'yan sandan kasar janar Kale Kayihura wanda ya shaidawa manema labarai yayin wani samame na muamman da 'yan sandan suka kaddamar a gundumar Jinja da ke gabashin kasar, ya kara da cewa, 'yan sanda na da cikakkun bayanai na gurfanar da Jamil Mukulu a gaban kotu.
Janar Kayihura ya ce, an shafe kusan shekaru 20, ana neman Mukulu, lamarin da ya tilastawa 'yan sandan kasa da kasa gabatar masa takardar sammaci, kana kwamitin sulhu na MDD ma ta ayyana shi a matsayin mutumin da ake nema ruwa a jallo.
Dakarun kungiyar Mukulu dai sun sha tayar da hankali a jamhuriyar demokiradiyar Congo mai makwabtaka da kasar Uganda, baya da sace mutane da sanya yara da suke yi cikin kungiyar.(Ibrahim)