in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta samu shaidun aikata ta'asa a Sudan ta Kudu
2015-07-01 10:46:41 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Sudan ta Kudu (UNMISS) ta samu kwararan shaidun keta hakkin bil-adama da suka hada da sacewa da kuma yin lalata da mata da 'yan mata da ake zargin dakarun SPLA da takwarorinsu masu dauke da makamai da aikatawa a fadan da ya barke a watan Afrilu a jihar Unity.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ya shaidawa manema labarai cewa, sun samu wadannan shaidu ne daga wadanda suka tsira daga hare-haren da ake zargin dakarun na SPLA da masu dauke da makamai daga yankin Mayom da kaddamarwa kan fararen hula, inda suka wawashe dukiyoyi tare da kona kauyuka, kana sama da mutane 100000 suka kauracewa gidajensu.

Rahotannin da tawagar ta UNMISS ta tattara sun nuna cewa, dakarun sun rika yiwa mata da 'yan mata fyade, kana suka kona wasu da ransu a cikin gidajensu.

A farkon watan Yunin wannan shekara ne hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta ba da rahoton cewa, fadan da ya barke cikin watanni biyu da suka gabata a jihohin Unity da Upper Nile na kasar Sudan ta Kudu ya yi sanadiyar raba sama da mutane 100000 da gidajensu. Baya ga wasu kimanin dubu 60 suka tsalaka kasashen Sudan, Habasha, Uganda da sauran kasashe a farkon wannan shekara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China