in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci dakarun Sudan ta Kudu da su dakatar da farwa fararen hula
2015-07-09 10:40:45 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya yi kashedi ga sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da dakarun 'yan adawar kasar, game da kaddamar da hare-hare kan fararen hula.

Mr. Ban wanda ya yi wannan jan kunne a jiya Laraba cikin wata sanarwa da kakakin sa ya fitar, ya ce, ya zama wajibi ga sassan biyu su fito fili su bayyana wa duniya haramcin kaiwa fararen hula farmaki. Ya kuma kara da cewa, wadanda suka karya wannan doka za su hadu da fushin shari'a.

Sanarwar dai na zuwa ne a jajiberin ranar da ake cika shekaru 4 da samun 'yancin kan kasar ta Sudan ta Kudu, biyowa bayan kuri'ar raba gardama da kaso 99 bisa dari na al'ummar kasar suka kada, game da ficewa daga kasar Sudan a ranar 9 ga watan Yuli na shekarar 2011. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China