in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan adawa sun bukaci da a rusa hukumar zabe a Cote d'Ivoire
2015-06-15 10:43:53 cri

Kawancen jam'iyyun adawa da ke neman kawo sauyi a kasar Cote d'Ivoire (CNC) ya bukaci a ranar Lahadi da a rusa hukumar zabe mai zaman kanta (CEI) da take zargi da nuna bambanci.

Hukumar zabe ta CEI a yadda take yanzu, ba ta da wani hurumun aiki domin tana tattare nuna bambanci sosai, lamarin da ke shaida cewa, an tsara shirya magudi a zabuka masu zuwa.

Ba mu yarda da wannan hukuma ba ko kadan, in ji kakakin kawancen CNC, Laurent Akoun, a yayin wani taron manema labarai.

Bangaren adawa ya shawarta a kafa hukumar zabe dake kunshe mambobin din din din da aka zabe su daga manyan mutane masu nagarta da adalci, da 'yanci da wadanda ba su tare da ko wace jam'iyya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China