Rundunar 'yan sanda a Nigeriya ta ce, ta kame mutane biyu da ake zargin suke da hannu a hare-haren bama baman da suka auku a garuruwan dake wajen birnin na Abuja a ranar 2 ga watan nan da muke ciki.
Mutanen da ba'a bayyana sunayensu ba, dayan dai yana da shekaru 27, daya kuma 25, an kuma kama su ne lokacin da suke kokarin kai wani harin bam a Abuja, kamar yadda babban Sipetan 'yan sandan kasar Solomon Arase ya bayyana a ranar Talatan nan.
Mr Arase ya kuma ce, an gano wassu ababen fashewa 12 da suka boye su cikin gwangwanyen lemo da na'urorin tada bam guda 28 masu aiki da kansu a tare da wadanda ake zargi.
A kalla mutane 18 ne suka hallaka, wadansu 41 suka ji rauni a hare-haren bam da suka faru a garuruwan Nyanya da Kuje makonni biyu da suka gabata, wadanda kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram ta dauki alhakin kaiwa.
Kungiyar dai tana yaki da gwamnatin kasar ne a kan kudirinta na sai ta kafa na musulunci, dalilin da ya sa take ta aiwatar da hare-haren bama bamai ke nan, ya zuwa yanzu fiye da mutane 13,000 suka hallaka, wadansu da dama kuma aka sace su tun lokacin da kungiyar ta fara addabar jama'a a shekara ta 2009.(Fatimah)