Wani kamfe domin gudanar da zabuka cikin lumana a cikin watan Oktoba a kasar Cote d'Ivoire ya fara a dukkan fadin kasar a karkashin jagorancin wata kungiya mai zaman kanta. Shirin da aka ma taken "jan kati domin zaman lafiya, kafin da bayan zabuka cikin watan Oktoban shekarar 2015" a karkashin laimar "Tolerance in Word" wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Cote d'Ivoire.
Mun fara wannan kamfen cikin sauri domin kaucewa kasar Cote d'Ivoire sake fada wa cikin tashe tashen hankali, in ji kakakin kungiyar, Florent Kouame.
Cote d'Ivoire ta yi fama a shekarar 2010 da 2011, da rikici mafi muni wanda ya janyo zubar da jini cikin tarihin kasar, tare da yake yaken da ke da nasaba da zaben shugaban kasar na cikin watan Nuwamban shekarar 2010 da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalle dubu uku.
Tare da fadada ayyukanmu a fadin kasar, za mu yi kokarin fadakar da 'yan siyasa da kuma al'ummomi cewa, ba za mu fatan sake fadawa ba cikin irin wadannan matsaloli da tashe tashen hankali, in ji mista Florent Kouame. (Maman Ada)