in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gano wani sabon bincike kan mutanen da ke murmurewa daga Ebola
2015-10-16 10:27:32 cri

Kakakin majalisar dinkin duniya Farhan Haq ya bayyana cewa, wani binciken wucin gadi ya nuna cewa, kwayoyin cutar Ebola na ci gaba da rayuwa a jikin mutanen da ke dauke da cutar na tsawon watanni 9 ko da bayan sun rabu da cutar.

Haq ya bayyana hakan ne ga taron manema labarai a jiya, bayan da aka bayyana sakamakon binciken farko da aka wallafa, wanda ma'aikatun lafiya da tsaftar muhalli da kuma ta tsaron kasar Saliyo ta gudanar tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurka.

Kakakin na MDD ya kuma bayyana cewa, sama da maza 8,000 da suka murmure daga cutar a sassa daban-daban na kasashen Liberiya da Guinea da Saliyo suna bukatar fadakarwa da kulawar da ta dace, sannan kamata ya yi a rika yi musu gwaji daga lokaci zuwa lokaci, domin gano ko har yanzu cutar tana makale a cikin maniyinsu, kana su san matakan da ya kamata su dauka don gudun yada shi ga abokan zaman su.

Binciken ya nuna cewa, dukkan mazajan da aka gwada a watanni uku na farko bayan da suka kamu da cutar, an gano cewa, dukkansu suna dauke da cutar. Kana wadanda aka gwada bayan watanni 4 zuwa 6 bayan sun kamu da cutar, su ma an gano cewa, suna dauke da kwayar cutar.

Yanzu dai hukumar lafiya ta duniya WHO ta ba da shawara cewa, kamata ya yi a rika gwada miniyin mazajen da suka tsira daga cutar ta Ebola bayan watanni uku-uku da kamuwa da cutar. Sannan a rika yiwa wadanda aka gano suna dauke da cutar gwaji a ko wane wata har sai an tabbatar da cewa, babu kwayar cutar a cikin maniyinsu a bayan gwajin ko wane mako.

WHO ta kuma bayyana cewa, bincken da masana lafiya suka yi kan mutanen da suka murmure daga tsananin cutar Ebola, na nuna cewa, kwayar cutar na iya bulla a sassa daban-daban na jikinsu bayan wasu watanni masu yawa, kamar cikin idanu, maniyi, ruwan mama, cibiya da laka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China