Shugaba Al-Bashir wanda ya bayyana hakan a yau yayin bude zaman majalisar dokokin kasar na biyu, ya ce, matakin zai taikawa wajen kawo karshen matsayin yankin ta fuskantar tafiyar da harkokin mulki.
Shugaba na Sudan ya kuma lashi takwabin tabbatar da zaman lafiya a yankin Darfur da ragowar sassan kasar tare da tabbatar da cewa, mutanen da suka bar gidajensu sun koma matsugunansu.
Tun a shekarar 2003 ne yankin Darfur ke fuskantar yakin basasa. (Ibrahim)