in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tafka kazamin fada tsakanin sojojin Kamaru da mayakan Boko Haram
2015-10-21 10:14:22 cri

Wasu majiyoyin soja a kasar Kamaru, sun bayyana cewa, an tafka wani kazamin fada tsakanin rundunar sojojin kasar da mayakan kungiyar Boko Haram ta Najeriya a ranar Talata da yamma a Soueram, wani garin dake yankin arewa mai nisa na Kamaru dake kusa da iyaka da Najeriya.

Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun yi kutse a cikin wannan yanki na Kamaru dake kusa da wani wurin da aka jibge jami'an tsaro, inda nan take suka mai da martani ta hanyar harbe igwa kan abokan gaba dake kusanto su, in ji wadannan majiyoyi dake bayyana cewa, an tafka kazamin fada tsakanin bangarorin biyu, amma ba tare da ba da wani adadin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China