in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram ta kashe mutane 8 a Kamaru
2015-09-28 10:30:25 cri

Wasu mutane da ake zargi da 'yayan kungiyar Boko Haram ta Najeriya sun kai hari a ranar Asabar da yamma a Tika, wani kauyen dake yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru dake kusa da iyaka da Najeriya, inda suka halaka kusan mutane goma da kuma kona gidaje da dama, a cewar wasu majiyoyin soja a ranar Lahadi.

Harin ya faru ne a ranar Asabar da yamma da misalin karfe tara na dare. Mutane takwas suka mutu, dukkansu manoman Tika, wani karamin kauye mai tazarar kilomita 13 daga Hile Hifa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China