in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar MDD a CAR ta karbi karin korafe-korafe don gane da cin zarafin yara
2015-06-24 10:25:58 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a janhuriyar Afirka ta Tsakiya ko MINUSCA a takaice, ta ce ta karbi karin korafe-korafe, game da zargin cin zarafin yara kanana a kasar, wanda ake yiwa wasu sojojin kasashen waje dake aiki a kasar.

A ta bakin kakakin MDD Stephane Dujarric, tawagar ta MINUSCA ta ce rahotannin da ta samu sun nuna cewa, sojojin da ake zargi sun rika yin lalata da kananan yara a birnin Bangui, fadar gwamnatin kasar.

Dujarric wanda ke jawabi ga taron manema labaru, ya ce, idan har wannan zargi ya tabbata, ko shakka babu zai zamo wani babban laifi na karya ka'idojin MDD game da gudanar da ayyukan jin kai.

Wannan batu dai na zuwa ne a gabar da ofishin MDD mai aikin sa ido ko OIOS ya fidda wani rahoton bincike, game da zargin da ake yiwa wasu jami'an wanzar da zaman lafiya na keta hakkokin yara a Afirka ta Tsakiyar. Rahotan na OIOS ya bayyana cewa, akwai kwange cikin rahoton da aka gabatarwa MDD. Kana ba a baiwa wadanda irin wannan cin zarafi ya shafa tallafin da ya dace ba.

Sai dai Dujarric ya ce, a wannan karo MDD ta dauki matakan gaggawa game da zarge-zargen, kana an umarci kasashen sojojin da ake zargi, da su gagguata hukunta masu laifin, da zarar an tabbatar da gaskiyar zargin da ake musu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China