in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta janye ma'aikatanta daga Libya saboda barazanar tsaro
2014-07-15 14:15:08 cri

Wata sanarwar MDD ta ce, MDD za ta janye sauran ma'aikatanta daga kasar Libya, saboda dalilai na tsaro.

Sanarwar ta bayyana cewar, sakamakon fadan da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata, da kuma rufe filin jiragen saman kasa da kasa na kasar ta Libya da aka yi, hakan ya sa MDD ta yanke shawarar janye sauran ma'aikatanta, domin tabbatar da kariyar lafiyarsu da 'yancinsu na walwala.

MDD ta lura cewar, a halin da kasar ta shiga, babu wata damar ci gaba da gudanar da ayyukanta, na baiwa kasar shawarwari da goyon baya.

MDD ta yi nuni da cewar, janye ma'aikatan da MDD ta yi, wani mataki ne wanda ba na din-din ba, kuma ta ce, da zaran lamurran tsaro sun daidaita, za ta maido da ma'aikatanta.

A safiyar ranar Lahadi ne, kazamin fada ya barke, a babban birnin kasar Tripoli, a yayin da wasu kungiyoyin Islama masu dauke da makamai, suka kaddamar da hari a kan filin jiragen kasa da kasa na kasar, harin da suka kai ya shafi wasu muhimman hanyoyi, kuma an rufe filin jirgin saman a kalla na kwanaki 3.

A halin da ake ciki, arangamar da ake yi ta haddasa hallaka mutane 9, da kuma jikkkata wasu mutane 30, kamar yadda majiyar kiwon lafiya ta kasar ta Libya ta tabbatar.

A makon da ya wuce ne MDD ta janye fiye da kashi 60 bisa dari na ma'aikatanta daga Libya saboda dalilai na tsaro. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China