in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya kafa kwamitin bincike game da zargin cin zarafin yara a CAR
2015-06-23 09:54:08 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya sanar da kafa wani kwamiti mai zaman kansa, wanda zai nazarci matakan da MDD ta dauka, game da batun zargin da ake yiwa wasu dakarun kasashen waje da ba sa karkashin MDD, na cin zarafin yara kanana a janhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR.

Wata sanarwa da kakakin MDDr Stephane Dujarric ya fitar, ta rawaito Mr. Ban na cewa, sabon kwamitin zai duba zargin lalata da kananan yara, da shigar da su ayyukan soji, wanda ake yiwa wasu daga dakarun kasashen ketaren, lokacin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a Afirka ta Tsakiya.

Sanarwar ta kuma ce, tsohuwar babbar mai shari'a, ta kotun kolin kasar Canada Marie Deschamps ce za ta jagoranci kwamitin mai wakilai uku. Sauran mambobin kwamitin su ne babban mai gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta MDD game da rikicin kasar Rwanda Hassan Jallow, 'dan kasar Gambia, da kuma Yasmin Sooka, babbar darakta a asusun kare hakkokin bil'adama a kasar Afirka ta Kudu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China