in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawan dake zaune a Amurka sun yi allah wadai da ziyarar da firaministan Japan ya kai Yasukuni
2013-12-29 17:16:06 cri
Ran 28 ga wata, wasu shugabannin kungiyoyin Sinawa dake zaune a kasar Amurka sun yi taron kara wa juna sani a birnin New York, inda suka yi allah wadai da ziyarar da firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya yi a wurin ibada na Yasukuni. Sun bayyana cewa, za su ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Sin da ta yi suka kan ziyarar Shinzo Abe wurin ibadar nan na Yasukuni.

A wannan rana kuma, shugaban babbar kungiyar Sinawan dake zaune a gabashin kasar Amurka Liang Guanjun ya bayyana cewa, firaministan kasar Japan ya kai ziyara wurin ibadar nan na Yasukuni a ran 26 ga wata, ba tare da la'akari da damuwar kasar Sin da kasashe makwabtansa ba, wanda hakan ya sa Sinawan dake zaune a kasar Amurka suka yi allah wadai da wannan ziyara tasa.

Haka zalika, shugaban kungiyar Tsung Tsin Lv Jianqiang ya bayyana cewa, ziyarar Shinzo Abe wurin ibadar nan na Yasukuni ta saba da yanayin adalci da ka'idojin kasa da kasa, Sinawan dake zaune a kasashen ketare ba za su amince da ita ba, wurin ibadar Yasukuni dai wuri ne da kasar Japan ta kebe kaburburan masu laifukan yakin duniya na biyu, ziyarar firaministan kasar Japan ta nuna rashin girmamawa na kasar Japan ga kasashen da yakin ya shafa, da kuma aniyar kasar Japan na nuna yabo ga wandanda suka yi laifi cikin yakin.

Bugu da kari, a ran 28 ga wata, wasu kafofin kasar Japan sun sharhi kan ziyarar Shinzo Abe wurin ibada na Yasukuni.

Jaridar "Tokyo Shimbun" ta ruwaito maganar tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar LDP Taku Yamasaki cewa, Shinzo Abe ya kai ziyara a wurin ibada na Yasukuni ba tare da la'akari da moriyar kasar Japan, hakan zai haddasa sabani tsakanin kasar da gamayyar kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China