in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta zargi ziyarar da 'yan majalisar Japan suka yi a haikalin Yasukuni
2013-04-23 16:56:27 cri
'Yan majalisur dokokin kasar Japan 168 sun kai ziyara haikalin Yasukuni cikin tarayya a yau Talata 23 ga wata, game da batun, a yau ma kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying a nan birnin Beijing ta kalubalanci kasar Japan da ta nemi gafara kan harin da ta kai wa sauran kasashe, kada kuma su kara aikata ayyukan da za su janyowa sauran kasashe da ma kanta lahani, wadanda kuma za su iya ware ta a duniya.

Hua ta jaddada cewa, yadda kasar Japan ke fuskantar tarihi, da wannan ziyara a haikalin Yasukumi, wassu abubuwa ne da kasashen dake makwabtaka da ita a Asiya da kasashen duniya suke amfani da su don fahimtar hanyar da Japan za ta bi a nan gaba. Sai dai ya kamata Japan ta koyi darasi daga tarihi ta yadda za ta iya fuskantar nan gaba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China