in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mutane a kalla 17 a Najeriya yayin wasu sabbin hare-hare
2015-07-23 09:54:04 cri

Rahotanni daga jihohin Gombe da Plateau dake tarayyar Najeriya, na cewa, a kalla mutane 17 ne aka tabbatar da rasuwarsu, biyowa bayan wasu sabbin hare-hare da aka kaddamar a jiya Laraba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gombe Fwaje Atajiri, ya shaida wa majiyarmu cewa, wasu mahara sun hallaka mutane 9, baya ga wasu da dama da suka ji raunuka, yayin wasu hare-hare 2 da suka kaddamar. Ya ce, tuni aka garzaya da gawawwakin wadanda suka rasu zuwa asibitin kwararru na gwamnati dake birnin na Gombe.

A jihar Plateau wadda ke tsakiyar Najeriya kuwa, mutane 8 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu, a wasu hare-hare biyu da suka auku a karamar hukumar Barkin Ladi duka dai a jiyan.

Ganau sun bayyana cewa, an hallaka mutum guda a cikin gidansa, sai kuma wasu mutane 3 da aka yiwa kwantan bauna, yayin da sauran mutanen 4 suka rasu a yayin da aka kai musu hari a wata mashaya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China