in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama zai tura dakaru 300 zuwa Kamaru
2015-10-15 10:34:17 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, a ranar Larabar nan ya bayyana cewa zai tura wata tawagar dakaru kimanin 300 zuwa kasar Kamaru domin su gudanar da aikin binkice na kwararru a yankin.

Shugaba Obama, ya ce, da farko an tura jami'an soji 90 ne a Litinin, amma ana sa ran adadin jami'an zai karu zuwa 300.

Ya ce, jami'an za su ci gaba da kasancewa a yankunan kasar Kamaru ne, domin aikin samar da tsaro, har sai zaman lafiya ya wanzu a yankunan kasar.

A yayin taron manema labaru a ranar Larabar nan, mai magana da yawun fadar Amurka ta White House Josh Earnest, ya ce, dakarun za su gudanar da aikin ne a kan iyakokin kasar ta Kamaru domin dakile hare haren kungiyar Boko Haram, da ma sauran kungiyoyin tada kayar baya a yammacin Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China