in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya tabbatar da kisan dan Amurkan da IS ta yi garkuwa da shi
2014-11-17 10:27:55 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama a jiya Lahadi ya tabbatar da kisan 'dan Amurken nan Peter Kassig da kungiyar IS ta yi garkuwa da shi.

A cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar, Obama ya ce, Kassig, ma'aikacin sa kai, 'dan kasar Amurka, an dauke shi ta hanyar tsananin mugunta na kungiyar ta'addanci da gaba daya duniya ta danganta da rashin imani.

A wani hoton bidiyon da kungiyar ta fitar, ya nuna wani mai sanye da bakaken kaya da fuskarsa a rufe yana tsaye a kusa da wani kan mutum da aka fille, yana cewa, wannan kan Kassig ne. Hoton har ila yau ya nuna yadda ake fille kawunan sojojin Syria da yawa wadanda aka kama.

Shugaba Obama ya jinjina wa marigayi Kassig, yana mai kiran shi jarumin da ya yi aikin ceton rayukan jama'ar Syria da suka ji rauni suka kuma rasa muhallansu saboda tashin hankalin dake faruwa a kasar. Ya ce, ayyukan da ya yi ya nuna matsayin shi na sadaukar da kai domin kula da rayuwan jama'ar Syria.

Peter Kassig shi ne mutum na 3 'dan Amurka da kungiyar IS ta kashe a cikin watanni 3, tun da farko ta kashe wassu 'yan jarida biyu James Foley da Steven Sotloff. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China