Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi kira a ranar Talata kan ci gaba da kokarin da kawance domin kai hare-hare kan mambobin kasar musulunci ISIS a Syria. Obama ya yi wadannan kalamai a cikin jawabin da ya gabatar a ranar Talata a fadar White House kafin ya je gudanar da jerin tarurruka a MDD dake birnin New York.
Da farko a cikin wannan wata, na gabatar wa al'ummar Amurka shirinmu na yaki da barazanar kungiyar ta'addanci da aka fi sani da ISIS ta kasar musulunci a Iraki da Levant, in ji shugaba Obama tare da ci gaba da cewa, ya bayyana karara albarkacin wannan dama cewa, a cikin wannan kamfen, Amurka za ta gudanar da kai hare-hare kan cibiyoyin ISIS dake Iraki da kuma Syria, ta yadda wadannan 'yan ta'adda ba za su samu mafaka ba a ko'ina. (Maman Ada)