in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya yaba wa shugabannin Najeriya bisa ga shirya zabe cikin lumana
2015-04-02 10:45:55 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yaba wa shugaban kasar Najeriya mai barin gado Goodluck Jonathan da zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba kan dattakun da suka nuna na kaucewa duk wani tashin hankali a lokacin yakin neman zabe.

Kwanakin baya baya sun nuna wa duniya hadin kan 'yan Najeriya wuri daya kan niyyar kasar ta martaba tsarin demokaradiyya, in ji shugaba Obama a cikin wata sanarwa.

'Yan Najeriya sun dauki niyyarsu tare kuma cikin lumana domin makomar kasarsu, a cewar shugaban Amurka.

Da yake kara taya al'ummar Najeriya da mista Buhari murna, shugaba Obama ya bayyana cewa, yana maza mazan ya ci gaba da aiki tare da sabbin shugabannin Najeriya kan muhimman batutuwan da ke shafar kasashen nasu biyu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China