in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chadi ta kaddamar da wani babban kamfen allurar yaki da cutar shan inna
2015-09-20 13:09:42 cri
Ministan kiwon lafiya na kasar Chadi Hissein Massar Hissein ya kaddamar a ranar Asabar a wata unguwar dake kudancin N'Djamena, hedkwatar kasar Chadi, da ranukan kasa na allurar yaki da cutar shan inna.

Kamfen zai kwashe kwanaki uku, kuma ya shafi kananan jarirai zuwa kanana yara masu watanni 59 dake cikin jihohin kasar goma sha biyu masu makwabtaka da kasashen Kamaru, Nijar, Najeriya, Afrika ta Tsakiya da kuma Sudan.

Kasar Chadi ba ta samu yaro ko guda ba da ya kamu da cutar shan inna tun a cikin watan Yunin shekarar 2012.

Domin kawar da cuta kwata kwata, gwamnatin ta shigar da wata sabuwar allura da za'a yi amfani da ita ta hanyar yin allura ga yara masu watanni uku zuwa watanni goma sha daya, tare da taimakon abokan hulda dake samar da tallafin kayayyaki da na kudi.

Babu wanda yake fatan ganin Chadi ta rasa cigaban da ta samu bayan gwagwarmayar da ta yi wannan fanni, in ji dokta Marchel Ouattara dake kula da cibiyar UNICEF a kasar Chadi.

Mista Hissein Massar Hisssein yayi kira ga dukkan bangarorin daban daban na kasar da su himmatu wajen yaki domin kawar da cutar shan inna daga kasar Chadi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China