in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma wata dokar yaki da ta'addanci mai cike da takadama a Chadi
2015-07-31 10:17:49 cri

A kalla makwanni uku bayan wani jerin hare haren kunar bakin wake da aka kai a N'Djamena, babban birnin kasar Chadi, 'yan majalisar dokokin Chadi sun amince a ranar Alhamis da wani shirin doka mai cike da takadama, dake bayyana aiwatar da hukunci mai tsanani ga masu hannu ko wadanda aka hada kai shi domin kai hare haren ta'addanci.

Dokar da ta shafi hukunci mai tsanani kan ayyukan ta'addanci, da aka amince da ita bayan kusan sa'o'i goma, ana tafka muhawara, na magana kan aiwatar da hukuncin kisa ga duk wani mutum da ya aikata harin ta'addanci, ko taimaka da kudi ko neman daukar mutane, ko ma baiwa mutane horo domin su kai hare haren ta'addanci.

Shirin dokar na farko da aka kai gaban gwamnati ya tsai da hukuncin daurin rai da rai a matsayin hukunci, amma kuma alkali ya bayyana cewa, wannan hukunci yana da sassauci sosai, domin haka ne aka maye gurbinta da hukuncin kisa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China