Ministar ma'aikatar sadarwa a tarayyar Najeriya Omobola Johnson, ta ce, gwamnatin kasar za ta dauki kwararan matakan hukunta kamfanonin wayar sadarwa, da suka gaza ba da hidima mai nagarta ga al'umma.
Omobola wadda ta bayyana hakan a birnin Ikko, yayin wani taron manema labaru, ta ce, tuni ma'aikatarta ta fara wani shirin hadin gwiwa, da hukuma mai ba da kariya ga al'umma a sashen ba da hidima, domin ja wa kamfanonin sadarwar da suka gaza sauke nauyin dake wuyansu birki.
Ministar ta ce, akwai zargin yankewa abokan hulda kudade ba tare da ba da hidima ba, da rashin samun cikakkiyar hidima, da tallata wasu hidimomin bogi, da ake wa wasu kamfanonin sadarwar kasar. Hakan a cewarta, ya sanya a baya, aka ci tarar wasu kamfanoni makudan kudade sama da naira miliyan 1700, amma har zuwa yanzu ba ta sauya zani ba.
Da take zayyana matakan da ake dauka domin kyautata harkokin sadarwar tarho a kasar, Omobola ta ce, yanzu haka ana kokarin hadin gwiwa da gwamnatocin jahohin kasar domin ragewa kamfanonin sadarwar nau'o'in haraji da suke biya. Har ila yau, majalissar zartaswar kasar ta amince da kudurin doka, da ya tanaji hukunci mai tsauri ga masu haddasa matsala ga hanyoyin sadarwar kamfanonin ta yanar gizo. (Saminu)