Adadin wayoyin salula dake shiga kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara zai karu daga kashi 52 cikin 100 a shekarar 2012 zuwa kashi 79 cikin 100 a shekarar 2020, a cewar wani sabon rahoton da wata cibiyar binciken kasa da kasa ta fitar a ranar Laraba.
Rahoton na Frost and Sullivan ya nuna cewa, adadin sadarwa ta wayoyin salula bisa dogon zango kamar yadda wasu hasashe suka nuna zai cimma miliyan 160 a shekarar 2016, wanda ya haura har sau hudu da na shekarar 2012.
Shigowar wayoyin salula da ake samu cikin farashi mai rahusa, wadanda kuma aka kera musammun ma domin kasuwar Afrika, ta kyautata hasashen wannan kasuwa, in ji Joanita Roos, wata mai fashin baki ta bangaren fasahohin sadarwa a cibiyar Frost and Sullivan. Wannan alfanu na bayyana sauye sauyen da ake samu na zaman rayuwar mutanen Afrika dake amfani da salula, musammun a yayin da suke yin amfani a karon farko da internet ta wayoyin salularsu, in ji madam Roos. Kasuwar wayoyin salula a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara na kasancewa wata muhimmiyar dama ga kamfanonin sadarwa, da kamfanonin dake kera wayoyi, mahaja da sauran kayayyaki wajen bunkasa harkokinsu, in ji wannan rahoto. (Maman Ada)