Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya fada a ranar Alhamis cewar, zai hada kai da takwaransa na kasar Sudan Omar al-Bashir domin samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Shugabannin biyu sun yi wata gajeriyar tattaunawa ne a filin sauka da tashin jiragen samar Sudan, inda suka tattauna batun karfafa danganta a tsakanin kasashen biyu.
Kenyatta ya shedawa 'yan jaridu cewar, sun yi ganawar ne domin tattauna yadda za su karfafa dangantaka dake tsakanin kasashen nasu da kuma ciyar da kasashen biyu gaba.
Ya kara da cewa, kasashen Kenya da Sudan makwabtan juna ne, a don haka akwai bukatar su tattauna yadda za su ci gaba da kasancewa aminan juna da kuma bunkasa ci gaban kasashen biyu.
Haka zalika Kenyatta ya ce, ya tattauna da al-Bashir kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen nasu, musamman kan batun zaman lafiya da tsaro. (Ahmad Fagam)