Kasar Sin ba za ta samu saurin bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata ba, sai dai ta ci gaba da yin gyare-gyare a gida, kamar yadda Jim Yong Kim, shugaban bankin duniya ya fada a ranar Talata 8 ga wata, yayin da yake ziyara a nan kasar Sin.
A yayin taron manema labaru da aka shirya a Beijing, mista Kim ya yaba wa kokarin da kasar Sin take yi a fannonin sauya hanyar bunkasa tattalin arziki da neman samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Ya kara da cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin dogo da matsakaicin lokaci na yin babban tasiri kan tattalin arzikin duniya. Sin ba za ta samu saurin bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata ba, sai dai ta ci gaba da yin gyare-gyare a gida. Yanzu haka kasar Sin tana kan irin wannan hanya, kuma ta samu ci gaba mai kyau.
Ban da haka, mista Kim ya yi maraba da yadda kasar Sin take goyon bayan kafa bankin zuba jari kan ababan more rayuwar jama'a na Asiya da bankin raya kasashen BRICS, inda ya ce, babu wata takara a tsakanin bankin duniya da wadannan sabbin bankunan da ya kira abokai, kuma su ba abokan gaba ba ne. A shirye yake wajen amfani da kwarewa da fasahohi mafi nagarta da ya samu daga wadannan sabbin abokai, tare da ba su goyon baya, a kokarin taimaka musu wajen inganta ababen more rayuwar jama'a a kasashe masu tasowa. (Tasallah)