Kasar Tunisia ta gargadi 'yan kasarta da su kauracewa bulaguro zuwa kasar Libya musamman saboda tashin hankali a kusa da kan iyaka kasar da Libya.
Wasu wadanda ake yin tashin hankalin a idanunsu sun ce, a ranar Lahadi an kashe wadansu 'yan kasar Libya guda 2 a kan iyaka ta Ras Jedir.
Rahotannin kafofin yada labarai sun ba da tabbaci cewar, sojoji masu biyayya ga janar Khalifa Haftar mai ritaya sun kai hari a Boukamech, garin dake kusa da kan iyakan Tunisia da Libya daga kudu maso gabashin kasar.
Wadanda aka yi abin kan idanunsu a garuruwan Ben Guerdane da Zarzis sun tabbatar cewar, sun ji karan fashewar wasu abubuwa da kuma karan faduwar bindiga mai linzami daura da kan iyaka na Ras Jedir.
A halin da ake ciki, yankin kan iyaka ya zamanto wurin kai hare-hare, kuma hakan ya sa hukumomin Tunisia daukar mataki na samar da dakaru a kan iyaka domin kare kan iyakar kasar. (Suwaiba)