Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya fara wani rangadin aiki a ranar Alhamis a kasashen Afrika uku da suka hada da Guinea-Equatoriale, Nijar da kuma Senegal, a wani labarin da hukumomin kasar suka bayar a ranar.
A cewar cibiyar kula da hulda da 'yan jarida ta fadar shugaban kasar, shugaba Conde ya bar birnin Conakry a ranar Alhamis domin isa Malabo, zangon farko na wannan rangadi nasa a wannan shiyya, inda zai halarci bikin samun 'yancin kasar Guinea-Equatoriale a ranar 3 ga watan Agusta.
Daga bisani, shugaban Guinea, zai isa Niamey a ranakun 4 da 5 ga watan Agusta, inda zai halarci wani zaman taro kan tsaro a yankin shiyyar yammacin Afrika da ingiza tattalin arzki bayan matsalar Ebola.
Sai kuma a ranakun 6 da 8 ga watan Agusta a birnin Dakar, mista Alpha Conde da takwaransa na kasar Senegal Macky Sall za su tattauna batutuwan karfafa huldar dangantaka dake tsakanin kasashen Guinea Equatoriale da Senegal.
Kana zai tabo matsalolin da shiyyar take fama da su tare da shugaba Sall, da ke shugabantar kungiyar ECOWAS a wannan karon.(Maman Ada)