Kwamandan sojojin da ke kula ayyukan yaki da mayakan Boko Haram a garin Maiduguri da ke yankin arewa maso gabashin kasar Manjo Janar Yusha'u Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke bayani game da hare-haren kunar bakin wake na baya-bayan da aka kai a sassan kasar, hare-haren da ya ce, an kai su ne da nufin janye hankulan sojojin kasar daga irin nasarorin da suke samu a yakin da suke yi da 'yan ta'adda.
Kwamandan ya ce, babu abin da zai hana sojojin ganin bayan ayyukan ta'addanci a kasar kafin watan Disamba. Ya ce, tuni sojojin suka samu wasu bayanan sirri game da wadannan ke da hannu a hare-haren bama-baman da aka kai a birnin Maidugurui, fadar mulkin jihar Borno. Kuma yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike.
Don haka ya yi kira ga 'yan Najeriya, da su ci gaba da baiwa jami'an tsaro hadin kai don hana aukuwar hakan nan gaba. Ya kuma bayyana cewa, sojojin na kokarin bullo da dabarun da suka dace ta yadda jama'a za su rika baiwa hukumomin tsaro muhimman bayanai ba tare da kowa ya sani ba.(Ibrahim)