in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asibitocin gwamnati a Najeriya na kula da mutanen da suka jikkata a hare-haren Kuju da Nyanya
2015-10-06 14:20:05 cri
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, mutane 26 cikin 39 da suka jikkata sakamakon hare-haren bama-baman da aka kai a garuruwan Nyanya da Kuje na ci gaba da karbar jinya a asibitoci daban-daban da ke babban birnin tarayyar kasar.

Jami'in gudanarwa na hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya(NEMA) reshen Abuja Ishaya Chonoko wanda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin, ya kuma bayyana cewa, an sallami ragowar mutane 13 bayan da aka yi musu magani.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar ba ta samu wani rahoto ba cewa, asibitoci sun ki kula da mutane da suka jikkata, kamar yadda wasu kafofin watsa labarai ke yayata hakan.

Kimanin mutane 20 ne suka jikkata a harin na Kuje kana 19 a Nyanya, baya ga mutane a kalla 18 da aka ba da rahoton sun rasa rayukansu a hare-haren na ranar 2 ga watan Oktoba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China