Mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP Olisa Metuh wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ya bayyana hare-haren a matsayin dabbanci kana aikin matsorata.
Ya ce, jam'iyyar ta kadu matuka da samun labarin wadannan munanan hare-hare da suka yi sanadiyar rayukan bayin allah da dama.
Jam'iyyar ta ce, abin takaici an kai munanan hare-haren ne sa'o'i 24 bayan da kasar ta yi bikin cika shekaru 55 da samun 'yancin kai.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jam'iyyar PDP tana nuna alhininta game da ayyukan ta'addanci da ke ci gaba da faruwa, musamman a yankunan arewacin kasar, inda masu tada kayar baya ke ci gaba da yanka mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kowa ce rana.
Jam'iyyar ta kuma nanata kudurinta na goyon bayan manufofin shugaba Muhammadu Buhari na kawo karshen ayyukan ta'addanci a kasar.
Koda ya ke jam'iyyar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta kara mayar da hankali kan hanyoyin tattara bayanan sirri da daukar matakan soja kan ayyukan ta'addanci a kasar.
Bayanai na nuna cewa, mutane 18 ne suka mutu kana 41 suka jikkata sanadiyar bama-bamai ukun da suka fashe a Abuja.(Ibrahim)