Mutane 18 ne suka mutu sannan 41 suka samu raunuka a sakamakon tashin boma bomai har sau uku.
Babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA Mohammed Sani-Sidi, wanda ya jagoranci jami'an hukumar wajen daukar wadanda suka samu raunuka zuwa asibitoci, ya tabbatar da cewar gwamnati ta amince da biyan kudaden magungunan kyauta ga wadanda harin ya raunata.
Hukumar ta NEMA, ta ce mutane 15 ne suka mutu wasu 20 suka jikkata a harin na Kuje yayin da mutane 3 suka mutu sannan 21 suka jikkata a harin Nyanya dake kusa da birnin na Abuja.(Ahmed)