in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Xi Jinping a kasar Amurka ta inganta neman samun bunkasuwa da yin hadin gwiwar kawo moriyar juna cikin lumana
2015-09-29 14:10:32 cri

Daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Satumba na shekarar 2015 ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki zuwa kasar Amurka kana ya halarci jerin tarurukan koli na cika shekaru 70 da kafa MDD.

Bayan da shugaba Xi ya kawo karshen wannan ziyara, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi karin bayani game da wannan ziyara, inda Wang Yi ya bayyana cewa, ziyarar da Xi Jinping ya kai a wannan karo ta kasance ziyara mai matukar tarihi a wannan zamani

A cikin kwanaki 7 da suka gabata, Xi Jinping ya yi musayar ra'ayoyi tare da mutane daga sassa daban daban na kasar Amurka, sannan ya gabatar da muhimman jawabai da dama a birnin Seattle dake yammacin kasar Amurka da Washington DC cibiyar siyasar kasar da kuma birnin New York, cibiyar harkokin kasa da kasa. Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yaba matuka ga sakamakon da aka samu a yayin wannan ziyara, inda suke ganin cewa, wannan ziyara na da ma'ana sosai,kuma ko shakka babu, za ta yi tasiri matuka ga makomar kasashen biyu da kuma bunkasuwar kasashen duniya cikin lumana. Muhimmiyar ma'anar wannan ziyara ta shafi fannoni 3,

Na farko, ta zama misali ga kokarin kafa sabon salon hulda tsakanin manyan kasashe, da kafa kyakkyawar makomar hadin gwiwar kasashen Sin da Amurka.

Na biyu, ta yi kira da a kafa sabuwar hulda a tsakanin kasa da kasa domin inganta aikin neman samun bunkasuwa cikin lumana a duk duniya.

Na uku, ta zayyana yanayin bunkasuwar kasar Sin,ta yadda kasashen duniya za su kara fahimtar yanayin da kasar Sin take ciki a zahiri.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China