in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin ya ba da guraben karatu ga matasan Mozambique
2015-09-29 09:57:33 cri

Daliban kasar Mozambique guda 20 suka amfana da guraben karo ilimi da kamfanin Huawei na kasar Sin ya bayar kamar yadda ministar ma'aikatar kwadago da tsaron al'ummar kasar Victoria Diogo ta sanar a birnin Maputo a ranar Litinin.

Madam Victoria Diogo ta yi bayanin cewa, wannan wata dama ce ga matasan kasar ta Mozambique da suke kammala karatunsu a jami'o'i, tare kuma da samun damar rungumar fannin fasahar yada labarai da sadarwa.

Ta ce, a cikin nan da shekaru 2, 'yan Mozambique 100 ne za su amfana daga guraben ayyukan sanin makama a kamfanin, kuma kamar yadda kamfanin ya tabbatar da niyyar rike guda 50 daga cikin adadin, banda sauran damar ayyuka da kamfanin ya saba samarwa.

Ministar ta kara bayanin cewa, bayan guraben karatu da kamfanin ya bayar, har ila yau ya amince da samar da sanin makaman aiki na kwararrun musamman a kasar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China