in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin sadarwa na fadada kafofin hada hadar kudi a Mozambique
2015-09-01 09:50:18 cri

Gwamnan babban bankin kasar Mozambique Ernesto Gove, ya ce, kamfanonin sadarwa na wayar tarfo dake ba da hidima a Mozambique, na taimakawa wajen fadada hanyoyin hada hadar kudade a kasar.

Gove wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, ya ce, irin wadannan kamfanoni da suka hada da Mcel da Vodacom, na baiwa al'ummar kasar su kimanin miliyan 10 damar tura kudade daga asusun ajiyar banki, da gudanar da sauran hada-hadar cinikayya karkashin tsarin M-Pesa da M-Kesh wanda ake iya yi ta wayoyin salula.

Gwamnan bankin na Mozambique ya kara da cewa, wannan hidima da kamfanonin waya ke bayarwa ga 'yan kasar za ta fadada da kaso 2 bisa dari nan da shekara mai zuwa.

Ya ce, baya ga wadannan hanyoyi na wayar salula, gwamnatin kasar na kara yawan rassan hada hadar kudade a sassa da yankunan daban daban dake kasar, inda a yanzu al'umma ke da damar amfana daga irin wadannan cibiyoyi dake a gundumomi 65 cikin jimillar gundumomin kasar 128. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China