Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya nemi afuwar al'ummar kasar Mozambique, bisa rasuwar uku daga 'yan kasar, sakamakon tarzomar kin jinin baki da ta auku a kasarsa a 'yan makwannin baya.
Shugaban Zuma ya bayyana hakan ne jiya Laraba, yayin ziyarar aiki ta yini biyu da ya fara gudanarwa a kasar ta Mozambique. Zuma ya ce, babu wani dalili da zai ba da damar aikata wannan ta'asa, wadda wasu tsirarun 'yan kasarsa suka aikata, musamman ma idan aka yi la'akari da abota, tare da zumuncin dake tsakanin kasarsa da Mozambique.
Don haka shugaban na Afirka ta Kudu ya sake jaddada neman gafarar 'yan kasarsa bisa aukuwar wannan lamari, yana mai cewa, Afirka ta Kudu na martaba aminanta na kurkusa, ciki hadda kasar ta Mozambique.
Jagororin kasashen biyu dai sun amince da daukar karin matakan inganta yarjejeniyoyin da suka rattabawa hannu game da ci gaban kasashensu. (Saminu)