Babbar jamiyyar adawar kasar Mozambique Renamo ta ce za ta dau fansa na yunkurin hallaka shugabanta Afonso Dhlakama, amma ta ce za ta dau matakin ne a siyasance.
Rahotanni sun ce, Dhlakama ya sha da kyar, bayan samun raunuka da ya yi a lokacin da 'yan bindiga suka budewa tagawar sa wuta a daren Asabar din da ta gabata a taskiyar lardin Manica, sannan harin ya raunata magoya bayan jamiyyar ta Renamo 4.
Jam'iyyar ta Renamo, ta zargi gwamnati da daukar nauyin harin, zargin da babbar jamiyyar kasar Frelimo ta musanta.
A yayin gudanar da taron manema labarai a ranar Alhamis din nan, babban sakataren jam'iyyar ta Renamo Manuel Bissopo ya bayyana cewar, jam'iyyar za ta dau fansa kan harin da aka kai mata, ya kara da cewar, ba za su laminci irin wannan ta'addanci ba.(Ahmad Fagam)