in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shiga zagaye na 3 na tattaunawar da bangarorin Sudan ta Kudu ke yi
2015-01-06 09:57:52 cri

Rahotanni daga birnin Arusha na kasar Tanzaniya na cewa, yanzu haka an shiga zagaye na 3, a tattaunawar da bangarorin kasar Sudan ta Kudu ke yi da wakilan jam'iyyar CCM mai mulki a Tanzaniya, jamiyyar da ke matsayin mai shiga tsakani a shawarwarin.

Da dama daga mahalarta zaman dai na ganin akwai yiwuwar a cimma nasara a wannan karo, matakin da ka iya kaiwa ga warware rikicin siyasar da Sudan ta Kudun ke fuskanta.

A cewar daya daga wakilan bangaren 'yan adawa Gioy Jooyul Yoi, tattaunawar da aka fara a jiya Litinin, ta banbanta da wadda aka kammala a kasar Habasha, wadda ta mai da hankali kaco-kan kan batun kafa gwamnatin hadin gambiza.

Rahotanni sun bayyana cewa, baya ga wakilan bangarorin biyu, zaman na ranar Litinin ya samu halartar jami'ai daga jam'iyyar CCM, da wakilan ma'aikatar harkokin wajen kasar Tanzaniya.

Kafin zaman na wannan karo dai bangarorin biyu sun taba tattaunawa har karo biyu, cikin shekarar da ta gabata a kasar ta Tanzaniya, karkashin jagorancin tsohon firaministan kasar John Malecela.

Rikicin kasar ta Sudan ta Kudu dai ya kasance musabbabin rashin shigar kasar cikin kungiyar hadin gwiwar kasashen gabashin Afirka ta EAC. Baya ga asarar rayukan dubban jama'a, rikicin ya kuma raba kimanin mutane miliyan daya da dubu dari bakwai da gidajen su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China