Kasar Sin ta baiwa kasar Tanzania tallafin motocin musamman 50, da wasu kayan aiki iri-iri a matsayin gudummawar yakin da kasar ke yi da masu haramtacciyar sana'ar nan ta farautar namun daji ba bisa ka'ida ba.
A ranar Lahadi ne dai jakadan Sin a kasar Lu Youqing, ya mika motocin ga mahukuntan Tanzania, motocin da kimar su ta kai dalar Amurka miliyan 1 da dubu dari 3.
A madadin gwamnatin Tanzania, minista mai kula da ma'aikatar albarkatun kasa da yawon shakatawa Lazaro Nyalandu, ya gode wa Sin bisa tallafin kayan aikin. Nyalandu ya ce, za a raba kayayyakin ga ma'aikatan gadun daji dake sassan kasar.
Motocin dai na kunshe da na'urorin tantance bayanai da wurare na GPS, wadanda ka iya ba da damar kai daukin gaggawa a duk inda aka samu bullar masu farautar namun daji. (Saminu)