Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da kai hari kan jami'an tawagar wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur ta AU da MDD wato UNAMID, inda ya bukaci hukumomin kasar Sudan da su hanzarta binciko wadanda ke da hannu a kai harin domin hukunta su.
A wata sanarwa da ta fito daga mai magana da yawun shugaba Ban ta ce, sojan kasar Afrika ta Kudu guda ya rasa ransa, sannan wasu 4 sun samu raunuka a yayin musayar wuta tsakanin su da 'yan bindigar.
Lamarin dai ya faru ne a yankin Mellit dake daura da arewacin Darfur a yayin da jami'an wanzar da zaman lafiyar ke raka wata tawagar ma'aikatan UNAMID dake dauke da kayan aiki.
Ban Ki-moon, ya aike wa gwamnatin Afrika ta Kudu da iyalan wadanda harin ya rutsa da su sakon ta'aziyya, sannan ya yi addu'ar samun waraka ga wadanda suka jikkata.(Ahmad Fagam)