in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya damu kan karuwar hari kan ma'aikatar wanzar da zaman lafiya a Darfur
2015-04-28 10:11:16 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya damu matuka a kan karuwar harin da aka kai kwanan nan a kan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a karkashin hadin gwiwwar kungiyar AU da majalissar wato UNAMID, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga ofishin kakakinsa ke bayyanawa.

A cikin sanarwa, Mr Ban ya yi suka a kan hari sau biyu a jere da wadansu mutane dauke da makamai da ba'a tantance su ba a Kass, dake kudancin Darfur makon da ya wuce, abin da ya sa ma'aikatan majalissar guda 6 suka ji rauni, kuma 4 daga cikin maharan suka mutu bayan da ma'aikatan suka mai da martini domin kare kansu, kamar yadda sanarwar da kakakin ya sanya wa hannu.

Don haka magatakardar ya yi kira ga gwamnatin Sudan da ta tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu a wannan danyen aikin, tare da daukan duk matakan da suka wajaba domin hana sake aukuwar hakan, ko kuma wata barazana ga ma'aikatan majalissar dake Darfur, duk da cewar UNAMID din ta kaddamar da nata tawagar masu binciken.

Haka kuma magatakardar ya damu da rashin cikakken hadin kai da gwamnatin Sudan ke bayarwa na ganin ta magance wannan lamari, kamar yadda sanrwar ta yi bayanin a ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin Sudan ta musanta taimakon da aka nema a wajenta na jirgin sama domin daukan wani ma'aikacin majalissar, 'dan kasar Habasha da ya samu rauni a bakin aikinsa a Mujkar dake yammacin Darfur, abin da ya sa ma'aikacin ya mutu bayan 'yan awanni.

A game da hakan magatakardara MDD ya aika da sakon ta'aziyar shi ga gwamnatin kasar Habasha, da iyalin mamacin. Yana mai kira ga gwamnatin kasar Sudan da ta mutunta yarjejeniyar matsayin dakaru da ta rattaba wa hannu tare da MDD ta hanyar daga dokar kayyade inda dakarun majalissar za su iya aiki. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China