in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabbin mutane 78,000 suka rasa muhallansu a Darfur na Sudan
2015-06-11 10:50:45 cri

An yi kiyasin cewa, yanzu haka akwai sabbin mutane kusan 78,000 da suka rasa muhallansu a Darfur na kasar Sudan wannan shekara saboda fadan da ke wanzuwa tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan adawa, in ji mataimakin magatakardar MDD game da ayyukan zaman lafiya Edmond Mulet a ranar Laraban nan.

Ya ce, a cikin mataki na biyu na gwaggwarmayyar da gwamnatin kasar ke yi, an jawo karin adadin wadanda suka rasa matsugunnansu, sannan kuma ofishin hulda da harkokin jin kai ya samu rahotan wani karin mutane 130,000 a kan wadanda yanzu haka ba su da muhallan nasu a kasar, amma ba a kai ga tantance su ba.

Mr Mulet ya ce, yanayin tsaro a yankin na Darfur har yanzu ya tsananta, kuma babu wani ci gaba da aka samu mai karfi a ayyukan samar da zaman lafiya, yana mai nuni da cewa, a wannan shekarar kawai an samu karin tashin hankali cikin kasar da take ta jawo barkewar tashin hankali a kai a kai.

Kwamitin tsaron MDD ya kira taro a ranar Laraba domin tattauna da kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU, da kuma ofishin MDD dake Darfur UNAMID, wanda aka kafa shi a watan Yulin shekara ta 2007 da babban makasudin ba da kariya ga fararen hula, kuma ikon shi na aiki har nan da ranar 30 ga wannan wata na Yuni. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China