in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna damuwa kwarai game da yanayin tsaro a Darfur
2015-01-30 10:18:13 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya nuna damuwarsa kwarai game da tabarbarewar yanayin tsaro a yankin Darfur, kamar yadda kakakinsa Stephane Dujarric ya bayyana wa manema labarai.

Rahotanni sun nuna cewa, rikici ya sake barkewa tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da masu dauke da makamai na yankin Darfur, abin da ya yi sanadiyar mutane da dama rasa matsugunnansu, an kuma tabbatar wa MDD cewar, yanzu haka a kalla mutane 36,000 ne suka kaura daga gidajensu a Darfur din saboda wannan tashin hankali.

Mr. Ban a don haka ya bukaci gwamnati da masu adawa da ita da su kai zuciya nesa, su kuma sauke nauyin dake wuyan na cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba tare da bata lokaci ba, domin hana ci gaban rasa matsugunnai da wahalar da al'ummomin wajen ke fuskanta a kan wadannan mutane da suka rasa matsugunansu a yankin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China