Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi matukar Allah wadai da harin bama-bamai da aka kaddamar a wata kasuwa dake garin Maroua a janhuriyar Kamaru, lamarin da ya sabbaba rasuwar mutane 20, tare da jikkata wasu da dama.
Wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ta rawaito babban magatakardar MDDr na jan hankalin mahukuntan Kamaru, da sauran kasashen dake yankin da su hada kai da juna wajen kawo karshen barazanar da kungiyar Boko Haram ke yi ga rayukan fararen hula.
Ban ya kuma jaddada goyon bayan MDD ga Kamaru, da ma sauran kasashen dake fama da hare-haren 'ya'yan kungiyar. A daya hannun kuma, ya bukace su da su tabbatar da kiyaye dokokin jin kai na kasa da kasa, da hakkokin bil'adama, da kuma dokokin 'yan gudun hijiya.
Daga nan sai ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnati da iyalan wadanda harin na baya bayan nan ya ritsa da su, yana mai fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
A ranar Laraba ne dai wasu tagwayen bama bamai suka tarwatse a wata kasuwa mai cike da jama'a a garin Maroua dake yankin arewa mai nisa na janhuriyar Kamaru, harin da ake alakantawa da kungiyar Boko Haram mai sansani a Najeriya. (Saminu)