Sojojin Nigeriya a kwanan nan za su kaddamar da harin kare kai don kawo karshen ta'addanci a arewa maso gabashin kasar dake yammacin Afrika, in ji babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Kenneth Minimah.
Janar Minimah wanda ya bayyana hakan a birnin Fatakwal dake jihar Rivers a kudu masu gabashin kasar lokacin wani rangadi na yini biyu da ya kai sansanin na cibiyoyin sojin kasar.
A ranar Lahadin nan, Minimah ya bayyana cewa, a karkashin jagorancin shugaban kasar Goodluck Jonathan, soji ta samu babban cigaba wajen inganta rayuwar sojoji da cibiyoyin ayyukansu, ta yadda za su iya tunkarar kalubalolin tsaro a kasar.
Nigeriya, in ji shi, tana fuskantar kalubalolin tsaro masu yawa wadanda daya daga cikin su shi ne na 'yan ta'addan Boko Haram da yanzu haka suka hallaka dubban mutane da suka hada da mata da kananan yara tun daga shekara ta 2009. (Fatimah)