in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu tagwayen hare-hare sun hallaka mutane a kalla 25 a Najeriya
2015-07-17 09:47:43 cri

Rahotanni daga jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, a kalla mutane 25 ne suka rasa rayukansa, wasu sama da 30 kuma suka jikkata sakamakon wasu tagwayen hare-haren bam da aka kai a wata kasuwa a garin na Gombe.

Wani jami'in hukumar ba da agajin gaggauwa ta Najeriya (NEMA) wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce, ya ga gawawakin mutane 25 warwatse a wurin da fashewar ta faru. An kuma garzaya da sama da mutane 30 da suka jikkata zuwa asibiti domin a yi musu magani.

Wasu ganau sun shaida wa manema labarai cewa, an kai hare-haren ne da misalin karfe 6 na yamma, agogon wurin a daidai lokacin da jama'a ke tsaka da sayayyan shirye-shiryen karamar sallah.

Mazauna yankin dai na zargin mayakan Boko Haram da kai irin wadannan hare-hare kan fararen hula da ba su ji ba su gani ba, inda alkaluma ke cewa, ya zuwa yanzu mayakan na Boko Haram sun hallaka mutane sama da 13,000 sanadiyar hare-haren da suka kaddamar a Najeriya tun daga shekarar 2009.

Hukumomin Najeriya dai na neman goyon bayan yankuna da kasa da kasa don ganin an kawo karshen wannan aika-aika na kungiyar 'yan ta'adda da ke kokarin ganin an shimfida shari'ar musulunci a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China