Wata majiya ta shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, shugabannin kasashen Senagal, da Togo, da Jamhuriyar Benin da kuma Najeriya za su hallara a Ouagadougou, helkwatar Burkina Faso domin tattauna hanyoyin da za'a warware rikicin siyasar kasar biyowa bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi a makon jiya.
Shugabanin kasashen sun hada da Macky Sall na Senegal, da Thomas Boni Yayi na jamhuriyar Benin, da Muhammadu Buhari na Najeriya, sai kuma Faure Gnassingbe na kasar Togo.
A cewar sanarwar, shugabannin 4 za su yi bulaguron ne bayan sun kammala taron ECOWAS wanda ya gudana a ranar Talatar a Abuja da nufin lalibo bakin zaren don warware rikicin na Burkina Faso.
Rahotannin sun ce, tuni shugabannin sun isa birnin Ouagadougou da misalin karfe 7 na yammacin jiya Talatar, kuma sun samu rakiyar wakilin MDD da ke yammancin Afirka.(Ahmad Fagam)